Labarai

Buhari ya ruda Twitter: Ya kafa masu manyan dokoki kafin cire takunkumi

Buhari ya kafa wa Twitter sharudda kafin ya janye takunkumin da ya sanya masu

…dole sai sunyi rajista da Nigeria an basu lasisi sannan kuma dole sai….

Daga Manuniya

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta gindaya wa kamfanin Twitter dokoki da sharudda kafin ta dage dakatarwar da akayiwa kamfanin a Nigeria

Manuniya ta ruwaito Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad yana cewa cikin sharuddan da aka sanya sun hada da dole sai kamfanin Twitter yayi rajista da hukumar Nigeria,  sannan sai an bashi lasisi hade da ka’idojin Nigeria wadanda sai ya yarda zai bi su sau da kafa kafin a janye takunkumin da aka sanyawa kamfanin sada zumuntar.

Mista Lai ya bayyana haka ne yau Laraba a yayin taron majalisar zartarwar kasarnan wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button