Labarai

Za a rika yanke hukuncin kisa ga masu satar karfen jirgin kasa

Zamu nemi a rika yanke hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai ga masu satar karfen jirgin kasa

Daga Manuniya

Ministan Sufuri Rotimi Ameachi ya ce suna kokarin ganin an kirkiri wata doka a majalisar dokoki ta tarayya da zata tanadi hukuncin kisa ko daurin rai da rai ga duk wanda aka kama yana lalata ko satar ko yanke karfen ko kayan jirgin kasa.

Ameachi ya ce jirgin kasa na daukar akalla mutum 80 a kowane koci kana akwai koci 14 zuwa 20 a duk tafiyar jirgi kenan idan aka yanke titin jirgin kasan kuma yayi hadari Allah kadai yasan mutanen da zasu mutu don haka zasu nemi a rika yanke hukuncin kisa ga masu satar karafunan titin jiragen kasar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button