Labarai

BARA: El-Rufai ya dauki sabbin ma’aikata dubu Goma aiki

Daga Manuniya

Manuniya ta ruwaito Gwamnatin jihar Kaduna ta ce a shekarar 2020 kadai ta dauki sabbin ma’aikata da suka darar ma dubu 10 a fanin kiwon lafiya, harakar ilimi da sauransu.

A watan Nuwamba 2020 Asibitin Barau Dikko ya dauki sabbin likitoci da malaman jinya 283 wanda hakan ya kara yawan ma’aikatan kiwon lafiya a asibitin suka kai mutum 191, daga mitum 32 da Gwamnatin Elrufai ta tarar a 2015.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta dauki mutum 1,064 aiki sannan itama hukumar kula da asibitocin yara ta dauki sabbin ma’aikata har mutum 1,225 aiki.

Jami’ar the KASU kuma a 2020 ta dauki sabbin ma’aikata 159 aiki kana Kwalejin ilimi ta, Gidan-Waya, tana shirin kaddamar da sabbin ma’aikata 388 da ta dauka aiki.

A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan jihar Kaduna Muyiwa Adekeye ya fitar a yau Litinin ya kuma ce Gwamnatin El-Rufai ta dauki mutum 14 aiki a ma’aikatar ruwa ta jihar.

Muyiwa ya kara da cewa yanzu haka hukumar kula da malaman firamare sun kammala shirin daukar sabbin malamai fiye da dubu Bakwai a fadin jihar “Kuma Gwamnatin jihar Kaduna zata cigaba da daukar kwararrun ma’aikata domin cike gurbin da ake bukata” wato dai kenan za a kori wasu amma za acigaba da daukar wasu da suka fi kwarewa domin cigaban jihar Kaduna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button