Labarai

A hukumance daga yanzu HND daidai take da Digiri a Nigeria –inji Majalisar dokoki

Majalisar dokoki ta zartar da doka daga yanzu shaidar karatu ta HND daidai take da Digiri a Nigeria

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar da ta haramta nuna bambanci tsakanin babbar difiloma ta Higher National Diploma (HND) da kuma digiri na farko a ƙasar.

Jama’a da dama na ganin wannan abin ƙarfafa gwiwa ne ga ɗaliban kwalejojin fasaha wato Polytechnic.

Ƙudirin dokar na nufin daga yanzu za a daina bambance tsakanin ɗaliban da suka yi karatun digirin farko a jami’a da kuma waɗanda suka yi babbar difiloma a kwalejin fasaha na Polytechnic a wuraren neman aiki da sauransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button