Labarai

Twitter ta goge jawabin da Shugaba Buhari yayi kan masu neman raba Nigeria

Twitter ta goge jawabin Shugaba Buhari sannan tayi barazanar goge shafinsa kwata-kwata daga dandalin twitter

Daga Manuniya

Shafin sada zumunta na twitter ya goge jawabin gargadin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kan masu neman tada kayar baya da neman raba kasa.

Twitter ya goge gargadin wanda hakan ke nuna suna iya goge shafin shugaban na Nigeria kamar yadda suka goge na tsohon shugabn Amurka Donald Trump lokacin da yayi jawabai da suka saba ka’idar twitter.

Sai dai Gwamnatin Nigeria ta zargi kamfanin na twitter da hannu cikin zanga-zangar masu neman a raba kasa musamman na IPOP wato masu neman kafa kasar Biyafara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button