Labarai

Yan sanda sun kashe yan bidigar da suka kashe Ahmad Gulak a jihar Imo

Daga Manuniya

Rundunar yan sandan Jihar Imo ta ce ta samu nasarar ganowa tare da kashe yan bidigar da suka kashe Ahmed Gulak a wata musayar wuta da sukayi da yan bindigar a yammacin jiya Lahadi.

Kakakin rundunar yan sandan Imo, SP Bala Elkana, ya ce yan IPOP/ESN ne suka kashe margayin. Ya ce bayan da suka samu wasu bayanan sirri sai suka bi diddigin yan bindigar inda suka tarar dasu a daidai Afor Enyiogugu junction dake karamar hukumar Aboh-Mbaise inda suka tarar da yan IPOP/ESN din suna tsakar raba albasar da suka kwace a wata trelar albasa daga Arewa suna rarrabawa jama’ar gari. Da ganin yan sanda sai suka bude wuta

Bayan musayar wutar Manuniya ta ruwaito yan sandan sun kashe yan IPOP din su 6 kana wasu 4 sun ji munanan raunuka

Sanarwar ta kara da cewa an samu motoci 3 daga cikin motoci 5 da yan bindigar sukayi amfani dashi wajen kashe margayin. Sai dai 3 daga cikin motocin sun kone kurmus tare da yan bindigar su 7 a ciki.

Sannan yan sandan sun kwace bindigar Ak47 guda 3, da Pistol guda 1, da Magazines din Ak47 guda 5, da tarin harsasai na Ak47 da kuma kayan tsafe-tsafe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button