Labarai

Kwamitin majalisa ya karbi rahoton neman a raba Kaduna

Daga Manuniya

Kungiyar jama’ar kudancin Kaduna (SOKAPU) ta nemi kwamitin gyaran kudin tsarin mulki na Nigeria ya raba jihar Kaduna domin a samu zaman lafiya mai dorewa.

Manuniya ta ruwaito shugaban kungiyar SOKAPU, Jonathan Asake, ya gayawa kwamitin cewa kirkirar jihar Gurara (Gurara State) daga jihar Kaduna ta yanzu zai kawo karshen duk wata matsala da jihar ke fuskanta tun tsawon shekaru.
 
A cewar SOKAPU akwai kabilu fiye da 67 a kananan hukumomi 13 dake yankin kana kuma tana da fadin kasa da ya kai 26,000kmsq da kuma yawan mutane da suka tasar wa miliyan 5.1 ga kuma dumbin albarkatun kasa da yankin ke da su.
 
Masu neman a raba Kadunan sun bayar da misalin cewa girman Kudancin Kaduna yafi karfin fadin jihar Kano wacce ke da girman kasa 20,000kmsq. Amma a haka Kano ke da kananan hukumomi 44. Sannan yawan jama’ar kudancin ya fi na jihohi 21 na kasarnan.
 
Bincike ya nuna Kudancin Kaduna ke da kaso 60% na ma’aikatan Gwamnati a jihar. Amma kuma SOKAPU a jawabinta ta ce an danne barayin kudancin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button