Labarai

Dan sanda ne ya tarwatsa kansa dazu a Ebonyi ba dan kunar bakin wake bane

AN YANKA TA TASHI: Ashe Dan sanda ne ya tarwatsa kansa dazu a Ebonyi ba dan kunar bakin wake bane

Daga Manuniya

Rundunar yan sanda a jihar Ebonyi ta ce mutumin da ya tarwatsa kansa dazu a kusa da wata makarantar framare ba dan kunar bakin wake bane jami’in dan sanda ne da aka tura aiki na musamman a yankin da abun ya faru.


Kakakin rundunar yan sandan jihar Ebonyi Mrs Loveth Odah ta shaidawa manema labarai cewa mutumin dan sanda ne sunansa Mista Idi Aminu kuma daga MOPOL 32 yake. Sannan ta ce gurnetin dake jikinsa ne ya bude cikin kuskure shine ta tashi dashi amma ba bom bane kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

A dazu ne dai labarai ya karade cewa wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a kusa da wata makarantar framare mai suna Amizi Amangbala Primary School dake karamar hukumar Afikpo da aka fi sani da Eke Market

Rahotanni a dazu sun ce mutumin yayi nufin shiga makarantar ne amma masu tsaron makarantar suka hana shi shiga.

Misis Odah ta ce tuni sun kwashi gawar  margayi dan sandan zuwa mutuware.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button