Labarai

Ɗan ƙunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa da bam a Jihar Ebonyi

Ɗan ƙunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa da bam a Jihar Ebonyi

Daga Manuniya

Wani da ake zargin dan kunar bakin wake ne ya tarwatse bayan da abubuwan jikinsa suka fashe a lokacinda yake daf da shiga wata makarantar framare ta yara dake Ƙaramar Hukumar Afikpo a Jihar Ebonyi

Lamarin dai ya faru ne da safiyar yau Talata.

Wannan dai shine farkon harin Bom da aka samu a yankin kudancin kasar a tsawon lokaci kodayake ana yawan samun kai hare-hare tare da kashe jami’an tsaro da kuma ƙona ofisoshin ‘yan sanda a yankin.

Sai dai hukumomi na zargin ƙungiyar IPOB mai fafutikar kafa ƙasar Biafra a yankin da kai hare-haren.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button