Labarai

Majalisar dokoki zata soke shirin NYSC kwata-kwata a Nigeria

MENENE RA’AYIN KU: Majalisar dokoki zata soke shirin NYSC kwata-kwata a Nigeria

Daga Manuniya

Majalisar dokoki ta soma tattauna batun soke shirin yiwa kasa hidima wato NYSC saboda a cewar ta shirin bashi da wani amfani a yanzu.

Dama dai a zamanin mulkin soja Janaral Yakubu Gowon ne ta kirkiri shirin na NYSC a ranar 22 ga watan  Mayu, 1973, a karkashin dokar Decree No. 24 of 1973 a matsayin wata dama ta hada kan yan Nigeria tun bayan gama yakin basasa da akayi a ranar 6, Yuni, 1967 zuwa 15 Janairu, 1970.

Majalisar ta ce yanzu ana fama da rashin tsaro a kasar kana kuma kamfanonin Gwamnati da masu zaman kansu basa daukar  masu bautar kasar koda an tura su sai yan tsiraru dake da kafa a Gwamnati ko wata alfarma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button