Labarai

Buhari ya yiwa matan sojoji ta’aziyya ta wayar tarho ya kuma bayar da hutun makoki

Buhari yayi wa matan sojojin da suka mutu ta’aziyya ta wayar tarho ya kuma bayar da hutu domin zaman makoki

Daga Manuniya

Gwamnatin tarayya ta baiwa sojoji hutun yau Litinin domin yin zaman makokin mutuwar Shugaba sojoji na Nigeria Laftanar Janaral Ibrahim Attahiru da tawagarsa su 10 da suka mutu a hadarin jirgin sama.

Kazalika Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci a sauko da tutar Nigeria kasa-kasa na tsawon kwanaki 3 (Litinin 24 zuwa -26 Mayu 2021) domin girmama mamatan.

A wani labari makamancin wannan kuma Shugaban kasar ya kira matar Shugaban hafsan sojin a waya yayi mata ta’aziyya bisa rasuwar mijin nata da sauran matan da suka rasa mazajensu a hadarin jirgin saman.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button