Labarai

Yan bindiga sun kashe Direban Sarkin Birnin Gwari sun kona motarsa

Yan bindiga sun kashe Direban Sarkin Birnin Gwari sun kona motarsa

Daga Manuniya

Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kashe Direban Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubair Jibril Mai Gwari ll, sun kona motarsa a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Manuniya ta ruwaito Direban mai suna Alhaji Nasiru Sarkin Zango, ya tafi Kaduna ranar Asabar shi kadai yayi wa motar Sarkin gyara inda a hanyarsa ta dawowa Birnin Gwari ne ya gamu da ajalinsa a daidai dajin Unguwan Yako .

Rahotanni sun nuna dama a daidai wajen ne yan bindiga suka taba budewa tawagar Sarkin wuta amma Allah ya tsare baya ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button