Janar Attahiru ya kama hanyar murƙushe Boko Haram Allah ya dauki ransa-inji Zulum
Daga Manuniya
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce shugaban Sojin Nigeria Laftanar Janar Attahiru ya kama hanyar kawo ƙarshen Boko Haram Allah ya karɓi ransa a hadarin jirgin sama.
Majiyar MANUNIYA ta ruwaito Gwamnan na cewa margayin sau shida yana kai ziyara jihar Borno tun bayan naɗa shi shugaban sojin Nigeria domin sa ido kan yadda ayyukan sojoji ke gudana a yaƙi da Boko Haram.
“Ya ziyarci rundunoni da dama na soja da ke fagen daga domin ƙarfafa masu gwiwa da kuma tabbatar da samun nasara,” in ji Zulum.
A yanzu haka ma dai ana kan rade-radin mutuwar Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
