in

ADC Shugaban hafsan soji yasa mahaifiyarsa ta shirya masa kayan buda baki suna hanya

ALLAH SARKI: ADC Shugaban hafsan soji ya kira mahaifiyarsa a waya yasa ta shirya masa kayan buda baki zasu shigo Kaduna kuma yana azumi

Daga Manuniya

Allah sarki kalli yadda mahaifiyar ADC (Dogarin) shugaban sojojin Nigeria Major Lawal Aliyu Hayat (LA Hayat) ta dafa kansa tana yi masa addu’ar fatan Alkhairi a lokacinda aka sanar da cewa shine zai zama sabon dogarin (ADC) sabon shugaban hafsan soji na kasa margayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

Manuniya ta ruwaito daga yan’uwan mamacin cewa ya kirawo mahaifiyarsu ya fada nata cewa zasu shigo Kaduna jiya don Allah ta hada mashi kayan shan ruwa don yana azumi.

Wajajen karfe 6 na yamma sukayi hadarin jirgi suka mutu a kusa da filin jiragen sama na Kaduna.

Karanta jawabin da shugaban sojin Nigeria yayi ana saura kwana 2 rasuwar sa

Janar Attahiru ya kama hanyar murƙushe Boko Haram Allah ya dauki ransa -inji Zulum