Amarya ta soka wa mijinsu mai mata 4 wuka ya mutu bisa zargin yayi wa wata cikin shege
Daga Manuniya
Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wata mata mai suna Olanshile Nasirudeen yar kimanin shekara 47 bisa zargin kashe mijinta Jimoh Nasirudeen ta hanyar soka masa wuka bisa zargin yayi wa wata mata ciki,
Manuniya ta ruwaito matar itace ta hudu a wajen mijinsu.
Kakakin yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis
Yace sun samu labarin wata mata ta soka wa mijinta wuka ranar Laraba a garin Ijebu-Ode
Manuniya ta ruwaito matar ta sokawa mijin nasu wuka ne a kafarsa har ta kai ga jijiyarsa ta yanke inda jini yayi ta kwarara har ya rasu bayan an kwashe shi zuwa babban asibitin garin Ijebu-Ode.
DSP Oyeyemi yace da ganin haka sai matar ta gudu amma daga bisani yan sanda suka samu nasarar kamo ta a garin Mobalufon dake Ijebu-Ode.
Tuni dai akayi Jana’izar margayin kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.