Labarai

YANZU-YANZU: Babu wani jami’in Gwamnatina da zai je Abuja zama da NLC har sai an maido wutar lantarki a duka fadin jihar Kaduna –inji El-Rufai

YANZU-YANZU: Babu wani jami’in Gwamnatina da zai je Abuja zama da NLC har sai an maido wutar lantarki a duka fadin jihar Kaduna –inji El-Rufai

Daga Manuniya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya lashi takobin cewa daga shi har mukarraban Gwamnatinsa babu wanda zai je zaman tattaunawa da kungiyar kwadago ko Gwamnatin tarayya har sai TCN ta sakar wa al’ummar jihar Kaduna wutar lantarkin da aka tauye masu tsawon kwanaki.

El-Rufai a wata sanarwa da ya fitar ya yi zargin cewa rashin sanin hakki ne yasa Gwamnatin tarayya ta bari har yan kwadagon suka hana hukumar TCN ta kawo wuta kuma Gwamnatin tarayya ta zuba masu ido.

TCN dai itace mai bayar da wuta kafin jihohi su iya sarrafa ta, a baya mun kawo maku rahoton yadda TCN din ta ce ala dole zata dauke wuta saboda kungiyar kwadago ta shake mata wuya.

Sai dai Gwamnan ya sake nanata cewa babu wanda zai kafa wa Gwamnati sharadi akan abunda ita ke da hakkin juya shi. Gwamnan dai ya yi bakin kokarinsa wajen ganin an maido wuta a jihar Kaduna amma abun ya faskara ganin cewa Gwamnatin tarayya ce kadai ke da ikon baiwa TCN din umurni su bi kanan kuma kungiyar ma’aikatan wutar lantarki sunyi barazanar muddin shuwagabannin su suka yarda suka amshi umurni daga sama aka kawo wuta a garin na Kaduna to ba kakkautawa zasu dunguma yajin aiki duka kasar baki daya lamarin da yasa dole aka ki maida wutar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button