Labarai

KU FICE MANA A JIHA: Dandazon Talakawa a Kaduna na zanga-zangar adawa da Kungiyar Kwadago

YANZU-YANZU: Dandazon Yan Kaduna na zanga-zangar  korar yan Kungiyar Kwadago ta NLC su fice masu daga jiha “Basa so basa goyon bayan zanga-zangar”

Daga Manuniya

Tura ta kai bango a Kaduna domin kuwa yanzu haka Talakawan jihar Kaduna maza da mata da samari sun yi dandazo sun fito nuna goyon bayan Gwamnatin jihar Kaduna tare da bayyana cewa basa tare da yajin aikin da Kungiyar kwadago NLC ke yi a jihar.

A cikin wani bidiyo da ake haskawa kai tsaye an gano dandazon talakawan suna wake-waken “Basa goyon bayan NLC” su fita su bar masu jiharsu da dai sauran maganganu na nuna rashin yarda da zanga-zangar da NLC din ke yi yau rana ta 3 a jihar ta Kaduna.

Masu zanga-zangar sun taru a wajajen shateletalen dake gab da inda Kungiyar Kwadago ke tsaitsaiye suna tasu zanga-zangar.

Yanzu haka dai masu zanga-zangar na kara taruwa inda ake fargaban kada suyi taho mugama da yan kungiyar NLC masu zanga-zangar adawa da manufofin Gwamnatin jihar

Duba shafinmu na Facebook latsa nan ==>> https://www.facebook.com/1099889356779682/posts/3482736558494938/ domin ganin sauran hotunan masu zanga-zangar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button