Labarai

DA DUMI-DUMI: Kungiyar Kwadago NLC ta janye yajin aikin da take yi a Kaduna

DA DUMI-DUMI: Kungiyar Kwadago NLC ta janye yajin aikin gargadi na kwanaki 5 da take yi a Kaduna

Daga Manuniya

Manuniya ta ruwaito Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasa NLC Kwamaret Ayuba Wabba ya sanar da cewa sun janye yajin aikin gargadi na kwanaki Biyar da suke yi a jihar Kaduna domin shiga tattaunawar sulhu da zasuyi gobe Alhamis da ministan Kwadago a Abuja

Manuniya ta ruwaito Shugaban kwadago Ayuba Wabba da jagororin kungiyar ta NLC zasu hadu da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da mukarraban Gwamnatin jihar Kaduna da kuma Ministan kwadago a fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari Aso Rock da karfe 10 na safe.

Dama dai dazu Manuniya ta ruwaito maku yadda Gwamnatin tarayya a karkashin umurnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanya baki kan rikicin NLC da El-rufa’i

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button