Labarai

Buhari ya sa baki don kawo karshen rikicin NLC da El-rufa’i a Kaduna

Da Dumi-Dumi: A karshe dai Shugaba Buhari ya saka baki domin kawo karshen rikicin kungiyar kwadago NLC da Gwamnatin Kaduna ta El-rufa’i

Daga Manuniya

Gwamnatin tarayya a karkashin umurnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baiwa Ministan kwadago da ayyuka na kasa Sanata Chris Ngige umurni ya gaggauta shiga tsakanin Kungiyar kwadago ta NLC da Gwamnatin jihar Kaduna domin kawo karshen yajin aikin dake faruwa a Jihar.

Manuniya ta ruwaito tuni ministan ya turawa Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El Rufai da manyan mukarrabansa da kuma shugaban kungiyar kwadago, Comrade Ayuba Wabba da jagororin kungiyar ta NLC takarda yana gayyatarsu ofishinsa gobe Alhamis domin sulhu da shawo bakin zaren takaddamar dake faruwa na zanga-zangar.

Ministan ya ce za ayi zaman tattaunawar ce a ofishinsa karfe dake Sakatariyar Gwamnatintarayya a Abuja da karfe 11 na safe.

Manuniya ta ruwaito dama dokar kwadago ta Trade Disputes Act, CAP . T8, Laws of  Federation of Nigeria (LFN) 2004; ta baiwa Ministan dama ya jagoranci duk wata tattaunawa domin kawo sulhu a duk wata baraka da ta shafi kwadago ko maikatan a Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button