in

Zai kama shi: El-rufai na neman shugaban kungiyar kwadago ta NLC ruwa a jallo

YANZU-YANZU:  El-rufai na neman shugaban kungiyar kwadago ta NLC ruwa a jallo ya sanya kyauta mai tsoka ga duk wanda ya fadi inda yake

Daga Manuniya

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da sanya kyauta mai tsoka ga duk wanda ya bayar da bayani ko satar amsa akan inda shugaban kungiyar Kwadago na kasa Ayuba Wabba yake ko inda shuwagabannin kungiyar kwadago ta NLC suke a halin yanzu.

Manuniya ta ruwaito Gwamnan ya ce a gaggauta bayar da bayanin ga ma’aikatar shara’a ta jihar Kaduna domin Gwamnati zata dauki mataki akansa saboda ya take wata muhimmiyar doka.

Dama dai a jiya ne Gwamnan ya jaddada cewa batun kawo sauyi ba gudu ba ja da baya duk da barazanar da yan kungiyar kwadago ta NLC suke yi na yajin aiki, a cewar Gwamnan Gwamnatin jihar Kaduna ta tsaya a gefe tana daukar rahoton duk yadda zanga-zangar NLC ta kasance a jiya wanda suka yi ta taka doka da yiwa dokoki karan tsaye kuma dama yace da zaran sun gama tattara dokokin da kungiyar ta karya zai maka su a kotu.

Kadan daga cikin dokokin da suka taka wanda ya sabawa dokar yajin aiki shine sun shiga asibitocin mu sun kori mararsa lafiya da likitoci dake kula da su sun rufe asibitocin sannan sun tafi gidan wutar lantarki cen ma sun hana a baiwa jama’a wuta sun je sakatariyar jihar Kaduna sun kori ma’aikata sun rufe duk da cewa daga baya an fatattake su an bude kofar ma’aikata sun shiga sun yi aiki. Yan kungiyar kwadago ta NLC sun ga sun kasa tsaida harkokin Gwamnati sai suka koma bita da kulli da zagon kasa.

Gwamnonin PDP sun yi taro sun nemi a sauya fasalin kasa a kirkiri yan sandan jihohi, sannan a karawa Gwamnoni karfin iko

KADUNA: An tsinci gawar wata yarinya da akayi wa fyade ta dubura har ta mutu