Labarai

Wata Budurwa dake tafe tana latsa wayar salula ta fada rijiya ta mutu a Kano

Wata Budurwa dake tafe tana latsa wayar salula ta fada rijiya ta mutu a Kano

Daga Manuniya

Al’ummar jihar Kano sun shiga alhini sakamakon rahoton wata budurwa yar kimanin shekara 16 mai suna Amira da ta fada rijiya ta mutu sakamakon tana tafe tana danna wayar salula bata lura da rijiyar ba.

Majiyar MANUNIYA  ta ruwaito lamarin ya faru ne a garin Ja’en dake karamar hukumar Gwale a cikin jihar Kano.

Wani da abun ya faru a gaban idanunsa, Nura Ibrahim, ya bayyana cewa Amira da kawayenta su Biyu suna tafe suna hira margayiyar tana latsa waya hankalinsu baya wajen basu lura akwai rijiya a tsakiyar layin ba kawai sai dai suka ji ta fada rijiyar shine suka kwalla ihu muka ankara sai dai mun yi kokarin yin amfani da tsani domin mu ciro ta amma abun ya faskara.

Manuniya ta ruwaito daga majiyoyi cewa an yi kokarin kiran yan kwana-kwana domin su kawo dauki amma sai bayan awa Biyu suka samu isowa suka tsamo ta ko da aka duba lokacin ta rasu.

Kakakin hukumar kwana-kwana (hukumar kashe gobra) ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce cinkoson ababen hawa ne ya jawo jami’an su basu isa wurin da wuri ba har ta rasu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button