Labarai

KADUNA: An tsinci gawar wata yarinya da akayi wa fyade ta dubura har ta mutu

INDA RANKA: An tsinci gawar wata yarinya a Kaduna da akayi wa fyade ta dubura har ta mutu

Daga Manuniya

Wani abun tashin hankali ya faru a garin Kaduna bayan da aka tsinci gawar wata yarinya wani yayi mata fyade ta bayanta har ta mutu kafin ya jefar da ita ya gudu.

Manuniya ta ruwaito wata kungiyar sa kai a Kaduna karkashin Hajiya Rabi sun dauki yarinyar tare da yan sanda inda suka kaita asibitin Barau Dikko akayi ma gawar gwaje-gwaje domin binciken wanda yayi mata wannan mummunan aika-aika.

Bayanai sun ce yarinyar suna cikin wasa tare da kawayenta a wani gidan makawaftansu wajajen karfe 4:00 na yamma inda aka nemi yarinyar ko sama ko kasa, daga bisani Manuniya  ta ruwaito sai wajajen karfe 8:30 na dare aka yi kicibis da gawar ta a jejin kusa dasu wani ya yi mata fyade har ta mutu. ‘Da aka duba sai aka ga wanda yayi mata fyaden ta bayanta wato duburar ta yayi mata fyaden har ta mutu’

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button