Labarai

DA DUMI-DUMI: Sarkin Kano da wasu fasinjoji sun tsallake hadarin jirgin sama

Daga Manuniya

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da wasu fasinjoji a jirgin sama Max Air sun tsallake rijiya da baya bayan da jirgin da suke ciki daga Kano za su Abuja ya samu matsala a sararin samaniya minti 10 da tashin sa.

Majiyar Manuniya ta ruwaito jirgin ya tashi ne daga filin jiragen sama na Malam Aminu Kano International Airport, zuwa Abuja amma sai aka samu matsala inda ake zargin injin jirgin ya samu matsala da tashinsa.

Daily Nigerian ta ruwaito jirgin na Max Air mai lamba VM1645 ya kamata ace ya tashi zuwa Abuja tun karfe 1.30pm na rana amma aka sami jinkirin minti 30 wato sai karfe 2:00pm na rana ya tashi.

Daya daga cikinfasinjojin dake cikin jirgin mai suna, Dr Samaila Suleiman, ya ce ala dole sai da jirgin ya dawo kasa ya sauka bayan ya tashi da wajen minti 10. Yace hakan ya bata masu rai har ma wasu a cikinsu suka fasa tafiyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button