Labarai

Gwamnonin PDP sun yi taro sun nemi a sauya fasalin kasa a kirkiri yan sandan jihohi, sannan a karawa Gwamnoni karfin iko

Gwamnonin PDP sun yi taro sun nemi a sauya fasalin kasarnan, a kirkiri yan sandan jihohi, sannan a karawa Gwamnoni karfin iko

Daga Manuniya

Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta kiran taron gaggawa kan tsaro tare da Gwamnonin kasar nan domin tsara mafita game da sha’anin tsaron kasarnan.

Gwamnonin sun kuma bukaci a sauya fasalin kasarnan sannan a yi wasu gyare-gyare a kudin tsarin mulki. Sun kuma nemi a kirkiri yan sandan jihohi sannan a karawa jihohi karfin iko kana kuma a samarwa yan sanda da kayan aiki domin su yaki sha’anin tsaron kasar nan.

Manuniya ta ruwaito Gwamnoni sun gudanar da taron ne a Ibadan babban birnin jihar Oyo. Cikin Gwamnonin da suka samu halarta taron na yau Litinin sun hada da Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintini; da na Edo, Godwin Obaseki, da na Bauchi, Bala Mohammed sai kuma mataimakinsa Gwamnan Zamfara Mahdi Mohd wanda ya wakilci Gwamnan jihar, Bello Matawalle sai kuma Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.

Sauran Gwamnonin sun hada da na jihar Rivers Nyesom Wike; Akwa-Ibom, Emmanuel; Bayelsa Douye Diri; Benue, Samuel Ortom, da Gwamnan Enugu; Ifeanyi Ugwuanyi, da kuma na Delta Dr. Ifeanyi Okowa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button