Labarai

China na shirin janye dokar takaita haihuwa a kasar

Kasar China na shirin janye dokar takaita haihuwa

Daga Manuniya

Rahotanni daga kasar China na bayyana cewa kasar ta fara shirin janye dokar takaita haihuwa da ta saka a kasar domin baiwa kowane iyali damar haihuwar yara.

Manuniya ta ruwaito a karnin shekarar 1970 kasar ta kirkiri dokar iyali daya da daya kafin a 2016 suka sauya dokar zuwa iyali da ‘yaya biyu.

A kidayar shekarar 2020 kididdiga ta nuna al’umma na karuwa a kasar ta China sai dai Gwamnati ta ce sai ta kammala tsare-tsare yadda kasar ba zata cutu ba idan an janye dokar takaita haihuwar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button