Labarai

Ruwan sama mai karfi hadi da tsawa ya tarwatsa masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa

Ruwan sama mai karfi hadi da tsawa ya tarwatsa masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa yau a jihar Osun

Daga Manuniya

Ruwan sama mai karfi kamar da bakin kwarya hadi da tsawa ya tarwatsa zanga-zangar da wasu tsirarun kabilar Yarabawa ke yi yau asabar suna neman a raba Nigeria

Manuniya ta ruwaito zanga-zangar ta gudana ne a dandalin Nelson Mandela Freedom park ta wajajen tsohuwar garejin mota na Osogbo babban birnin jiharsa Osun.

Sai dai jim kadan da shugaban masu zanga-zangar Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya isa wajen taron ya hau saman mota domin fara jawabi kwatsam sai yanayin gari ya rikice inda hadari ya hadu nan da nan ya hanzarta jawabin da zai yi inda ruwan sama ya fara sauka kamar da bakin kwarya gami da tsawa da walkiya.

Cikin jawaban da Sunday Igboho yayi sun hada da cewar ba zasu bari ba ayi babban zaben shugaban kasa na 2023 ba a yankin jihohin Yarabawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button