in

Auren diyar Buhari da ICPC ke neman mijinta ruwa a jallo ya mutu

Badakalar Dala Miliyan 65: Auren diyar Buhari da ICPC ke neman mijinta ruwa a jallo ya mutu

Daga Manuniya

Fadar Shugaban kasa ta bakin Garba Shehu ya ce mutumin da hukumar yaki da manyan laifuka ta kasa, ICPC ke nema ruwa a jallo Gimba Ya’u Kumo bisa zargin wawure dala miliyan 65 ba surukin Buhari bane yanzu domin aurensa da yargidan Buhari Halima ya rabu tun shekarun baya.

Mista Kumo, tsohon shugaban Bankin, Federal Mortgage Bank, ya auri diyar Buhari ta biyu a watan October 2016 kuma Manuniya  ta ruwaito an daura auren ne a garin Daura, dake jihar Katsina.

Sai dai Garba Shehu ya ce tuni auren nasu ya mutu.

A yanzu haka dai hukumar ICPC na neman tsohon surukin Buharin ruwa a jallo da wasu mutane biyu bisa zargin waccen badakala ta dala miliyan 65.

Dubun wani matashi ta cika dake shigar attajirai a ‘social media’ yana gayyatar yan mata yayi masu fyade ya kashe su

An daga ranar rubuta jarabawar JAMB zuwa 3 ga watan Yuni 2021