Labarai

Sarkin Musulmi ya sake jaddadawa ba a ga wata ba sallah sai ranar Alhamis

DA DUMI-DUMI: Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta sake jaddada cewa ba a ga watan Sallah ba don haka hawan idi sallah karama a Nigeria sai ranar Alhamis 13 ga watan Mayu 2021. Kuma gobe Laraba za a tashi da Azumi.

Daga Manuniya

Biyo bayan watan sanarwa da shafi  Facebook na ganin wata na fadar sarkin Musulmin ta fitar jim kadan da jita-jitar sanarwar cewa Shehin malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi zai yi sallar idi gobe Laraba bayan da almajiransa suka tabbatar masa cewa sun ga jinjirin watan Shawal hakan tasa kwamitin ganin watan ya ce a gabatar masa da garuruwa da lambobin waya da sunayen mutanen da suka ce sun ga watan wannan sanarwa ta sa jama’a sun shiga zullumin ko majalisar sarkin Musulmin zata sake fitar da wata sanarwa.

To sai dai a bincike sahihi yanzu haka karfe 1:24 na dare duk wata majiya sahihiya daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi har zuwa fadar Gwamnatin jihars Sokoto sun ce zancen sanarwar farko da Sarkin Musulmi yayi tana nan daram bikin sallah a Nigeria sai ranar Alhamis.

“Yanzu haka da muke magana da ku an rufe fada mai alfarma Sarkin Musulmi ya shiga gida tun dazu don haka gobe Laraba za a tashi da Azumi”

Manuniya ta nemi jin ko me yasa shafin kwamitin ganin watan ya yi rubutu dazu bayan sanarwar farko ganin cewa hakan ka iya sa dar-dar ko tababa a zukatan yan Nigeria na cewa watakila a yanka ta tashi sai majiyar tamu ta ce “Ni dai na tabbatar maku a maganar gaskiya babu wata sanarwa da zata biyo baya, mai alfarma Sarkin Musulmi ya riga ya gama sanarwa ba a ga wata ba a Nigeria”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button