in

Sarkin Musulmi yace ba a ga watan Sallah ba a Nigeria Idi sai ranar Alhamis

DA DUMI-DUMI: Sarkin Musulmi yace ba a ga watan Sallah ba a Nigeria don haka idi sai ranar Alhamis

Daga Manuniya

Manuniya ta ruwaito Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayyana cewa a dubawar da akayi yau Talata ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Nigeria.

Yace don haka ranar Alhamis 13 ga watan Mayu ne za ayi sallar idi ta karamar sallah a Nigeria.

DA DUMI-DUMI: Ba a ga watan Sallah a Saudiyya ba don haka idi sai ranar Alhamis

DA DUMI-DUMI: An samu karin bayani daga gidan Sheikh Dahiru Bauchi kan batun ganin watan Shawwal 1442 A.H