Labarai

DA DUMI-DUMI: An samu karin bayani daga gidan Sheikh Dahiru Bauchi kan batun ganin watan Shawwal 1442 A.H

AN SABUNTA: Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce ayiwa Sarkin Musulmi biyayya a acigaba da Azumi Sallah sai ranar Alhamis kuma ya musanta labarin da ake yadawa cewa ya ce ayi sallah gobe Laraba

****Bayan kiraye-kiraye sunyi yawa Shehun ya bincika yace zai yi idi gobe….

A tattaunawa da Manuniya wasu makusantan Shehu sun tabbatar da cewa bara ne ya fitar da sanarwa kuma a wancen lokacin yayi sanarwar ne a cikin Bidiyo amma a bana bai yi ba, “saboda haka duk wanda ya ce Shehu yace a ajiye Azumi gobe to ya nuna maku hujja cikin bidiyo ko sautin murya”

Wannan dai ya kawo karshen kokarin amfanin da sunan Shehin malamin da wasu ke son yi wajen kawo rarrabuwa a addinin musulunci musamman kokarin tunzura wasu su ajiye Azumi Gobe bayan Sarkin Musulmi na Nigeria Alhaji Sa’ad Abubakar III ya tabbatar da cewa ba a ga watan sallah ba don haka ayi Azumi gobe Laraba sai ranar Alhamis ayi bikin idin sallah karama.

KARIN BAYANI///AN SABUNTA

Ga karin bayani daga gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi dangane da batun ganin watan Shawwal

Jim kadan da Manuniya ta tattauna da manyan majiyoyi guda biyu daga gidan Shehin Malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Wadanda duka suka bukaci a sakaye suna amma tabbas yan gidan ne) inda dukkanninsu suka karyata labarin da ake yadawa cewa Shehin Malamin yace a ajiye Azumi gobe Laraba ayi Sallar idi sabanin sanarwar Sarkin Musulmi na Nigeria. Daga bisani an kara samun karin bayani kuma…

Kwatsam kuma sai ga kira daga daya bangaren gidan Shehin Malamin inda suke jaddada cewa lallai lallai Shehin ya ce ayi Sallar idi gobe Laraba bayan an kai ruwa rana wajen tattaunawa bayan da wasu suka sanar da makusantar Shehun cewa sun ga wata a wajajensu.

Da Manuniya ta nemi su gabatar mata da sautin audio ko Bidiyo ko hoto dake nuna sahihancin maganar tasu sai cewa sukayi “A yanzu da muke magana daku muna gidan Shehu amma ya ce ba zai yi magana a cikin sautin murya ba wato ko audio ko Bidiyo amma dai tabbas ya fada yace gobe zai yi sallar idi”

Shima wani makusancin gidan Shehun ya ce “Lallai an samu rudani dazu wasu na cewa Shehu yace wasu na cewa bai ce ba amma dai tabbas ina mai baku tabbacin cewa Babangida A Maina mai kula da shafin sadarwar Shehu shi aka fadawa anga Jinjirin Watan Shawwal A Garin Bauchi, Gombe Da Azare kuma suka sanar da Shehu Dahiru Bauchi inda nan take yace ya sanarwa da Sarkin Musulmi a Sokoto da sauran wurare kuma ya bukaci a sanar da yan uwa amma shi ba zai sanar a hukumance ba don gudun sabani, amma tabbas “Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi RTA. Zai gudanar da Sallah Idi a gidansa dake hanyar Gombe zuwa Bauchi da misalin karfe 9:30 na Safe.” Inji majiyar a tattaunawarsu ta wayar salula da Manuniya

Manuniya batayi kasa a guiwa ba ta sake bin diddigin Babangida A. Maina wanda ya ce ayi magana ta chat. Amma dai ya tabbatar da labarin cewa Shehu zai yi sallar idi gobe Laraba.

ME KWAMITIN GANIN WATA NA FADAR SARKIN MUSULMI SUKA CE?

Kawo yanzu karfe 12:21 na dare Agogon Nigeria fadar sarkin Musulmi na Nigeria sun tsaya akan bakansu cewa ba a ga wata ba amma dai duk wanda yace ya ga watan to ya sanar dasu yanzu hadi da lambarsa da sunansa domin suyi bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button