Labarai

Yan fashi sun kai hari gidan Shugaba ma’aikatan Buhari dake Aso Rock

AN SHIGA UKU: Yan fashi sun kai hari gidan Shugaba ma’aikatan Buhari dake Aso Rock –inji fadar Shugaban kasa

Daga Manuniya

Fadar Shugaban kasa ta ce dagaske ne wasu yan fashi sun kai hari gidan Shugaba ma’aikatan Buhari, Ibrahim Gambari da misalin karfe 3 na daren yau Litinin,

Majiyoyi sun ce yan fashin sun fasa gidan Gambari dake kusa da fadar Shugaban kasa ta Aso Rock inda suka saci kaya iya san ransu sannan sukayi barnar da suke so a gidan sai kuma suka haura gidan wani babban jami’in kula da sha’anin mulki na fadar Shugabankasa, Abubakar Maikano inda a gidansa ma yan fashin suka ci karensu babu babbaka ba tare da an kama ko daya daga cikinsu ba.

Sai dai Manuniya ta ruwaito a wata sanarwa da kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya fitar da yammacin yau ya ce babu wani abun damuwa akai. Ya ce tuni an shawo kan lamarin.

Wannan lamari dai ya daga hankulan yan Nigeria na cewa lallai tabarbarewar tsaro ta kai inda takai tunda har ana iya kai hari fadar shugaban kasa sannan ma gidan shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa da kansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button