Labarai

Sarkin Musulmi ya ce a duba wata gobe Talata amma masana sun ce ba za a ga wata ba sai Laraba

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Saudi da Nigeria sun ce a duba watan Shawwal gobe Talata amma masana sun ce ba zai yiwu a ga wata ba sai ranar Laraba, kenan Azumi 30 za ayi

Daga Manuniya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta bukaci al’ummar musulmi su fara duban jinjirin watan Shawwal a gobe Talata 11 ga watan Mayu 2021 wanda ya zo dai-dai da 29 ga watan Ramadan

A wani labari makamancin wannan kuma shima mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III shima ya bukaci yan Nigeria su fara dubai jinjirin watan na Shawwal a gobe Talata.

To sai dai masana kimiyya da sararin samaniya sun ce ba shakka watan Ramadan sai ya kai 30, domin sun ce ba zai yiwu a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Talata ba, sunce sai ya kai Laraba domin za a kyankyashe jinjirin watan Shawwal da misalin karfe 8:00 na daren ranar Talata sannan sai a ga jinjirin wata a ranar Laraba 12 ga watan Mayu 2021.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button