Labarai

Ameachi ya kafa kwamiti su binciki Hadiza Bala tun daga hawan ta NPA a 2016

WATA SABUWA: Ameachi ya kafa kwamitin mutum 7 da zasu binciki Hadiza Bala Usman, ya umurce su suyi mata binciken kwa-kwaf tun daga hawan ta Shugabancin NPA a 2016 zuwa  lokacinda aka dakatar da ita

Daga Manuniya

Ministan Sufuri Rotimi Ameachi ya kafa kwamitin mutum 7 da zasu binciki Shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA, Hadiza Bala Usman wacce ya dakatar a makon da ya gabata

Mutanen sune Suleiman Auwalu a matsayin Shugaba sai Ben Omogo, a matsayin mataimaki.

Manuniya ta ruwaito sauran sun hada da Hussani Adamu, da Blessing Azorbo, da; Mercy Ilori, da; Muhly-deen Awwal, sai kuma Gabriel Fan wanda zai zama sakataren kwamitin.

Ameachi ya bukaci kwamitin su yiwa Hadiza Bala da hukumar ta binciken kwa-kwaf tun daga lokacin da ta hau mulkin hukumar a 2016 zuwa lokacinda aka dakatar da ita.

Ya ce yana son sanin me ya jawo ta soke kwangiloli a hukumar,  da ta soke su waye ta bamawa, yaya tayi nade-nade, yaya ta rika gudanar da ayyuka a hukumar, nawa hukumar ta samu a karkashin ta sannan nawa ta bayar ina da ina ta bi tsarin doka wajen aiwatar da ayyukanta sannan ina da ina ne ta take doka sannan kuma a karshe Ministan ya buƙaci kwamitin su bayar da shawarar me ya kamata ayi mata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button