Labarai

Kona ofisoshin yan sanda da kai masu hari hauka ne da rashin daraja -inji Buhari

ABUJA: Kona ofisoshin yan sanda da ake yi a wasu sassan kasarnan hauka ne da rashin daraja -inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ana rashin daraja a wasu sassan kasarnan ganin yadda takai ga har ana kaiwa cibiyoyin tsaro hari.

Daga Manuniya

Manuniya ta ruwaito Buhari ya jajantawa ilahirin iyalan da suka rasa iyalansu a sakamakon wannan abu da ya kira hauka na hare-haren ta’addanci dake faruwa a sassan kasarnan.

Sannan sai ya gargadi iyaye da shuwagabanni su tsawatawa matasa da ya’yansu su kiyayi bari ana amfani dasu wajen kaddamar da hare-hare da neman haddasa rikici da kalaman batanci.

Shugaban kasar ya ji takaicin cewa “to idan muka rika kaiwa jami’an tsaro hari wa zai kare mana rayuka da dukiyoyin mu anan gaba?”

Shugaban kasar ya kuma ce wannan karon ba zai je mahaifarsa ta Daura yin bikin sallah ba, kuma ba zai karbi gaishe-gaishen sallah ba kowa ya zauna a gidansa ya kula da dokokin annobar korona inji shugaban kasar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button