Labarai

ONDO: Yan fashi sun fatattaki yan sandan dake rakiyar wata motar kudi sun kwashe kudin

A JIHAR ONDO: Da rana tsaka yan fashi sun fatattaki yan sandan dake rakiyar wata motar kudi sun kwashe kudin

Daga Manuniya

Majiyar MANUNIYA ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na ranar Juma’a a kan babban titin Akure zuwa Ondo.

Ance motar na tsakiyar tafiya sai ga yan fashi su kusan 8 dauke da manyan makamai suna harbe-harbe inda nan take motoci biyu na yansanda dake rakiyar motar suka dirka kasa suka ranta a na kare domin ceton rayukansu

Bayanai sun nuna nan da nan yan fashin suka durafafi motar kudin da harbi har suka balle ta suka kwashe kudaden ciki sannan suka kara gaba.

Manuniya ta ruwaito shaidun gani da ido sun ce motar kudin ta fito ne daga cikin garin Ondo ta nufi Akure. Sun ce an harbi akalla mutum 4 har ma ana zargin dreba da wani dan sanda sun mutu a harin. Tuni dai jama’ar gari da masu babura suka ruga a guje sa’ilin da yan fashin suka budewa motar kudin wuta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button