Labarai

Muna tattaunawa da masu garkuwa domin ceto daliban jami’ar Greenfield –Inji Dr Ahmad Gumi

…malamin ya ce barayin sun fada masu sun fasa kashe daliban kamar yadda suka yi barazanar yi…

Daga Manuniya

Fitaccen Shehin Malami Dr Ahmad Gumi ya ce akwai alamun nasara zasu kubutar da ragowar daliban jami’ar Greenfield University dake Kaduna su 16, yace suna kan tattaunawa da barayin da suka yi garkuwa da daliban

Manuniya ta ruwaito Gumi na jawabi ne a lokacin da iyayen daliban kwalejin horas da aikin gona ta afaka su 27 da suka ziyarce shi domin yi masa godiya game da rawar da ya taka shi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wajen kubutar da ya’yan nasu.

Dr Ahmad yace barayin da suka sace daliban Greenfield University dake Kaduna sun gaya masa cewa sun fasa kashe daliban kamar yadda suka yi barazana a makon da ya gabata cewa zasu kashe su 16.

Shehin Malamin ya ce shi da Obasanjo suna taka rawa ne a matsayin masu shiga tsakani domin ganin barayin sun daina kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button