Labarai

Gwamnatin tarayya ta ce Jihohin 28 zasu fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a daminar bana

Gwamnatin tarayya ta lissafo Jihohin 28 da zasu fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a daminar bana

Daga Manuniya

Akalla jihohi 28 ne a Nigeria zasu fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a daminar bana inji Ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu

Adamu ya fadi haka ne a wajen taron nazari kan daminar bana da ambaliyar da ka iya faruwa a daminar shekarar 2021 da ya gudana yau Alhamis a Abuja.

Manuniya ta ruwaito Ministan ya lissafo jihohin dake cikin hadarin samun wannan mummunan ambaliyar sun hada da jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT Abuja da kuma, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano da jihar Kebbi.

Sauran sun hada da jihohin Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba da kuma Zamfara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button