Addini da RayuwaAlbum/EPHausa SongsHausa VideoKannywoodLabaraiWasanni

Da Dumi-Dumi: An ga watan Ramadan a Nigeria–inji Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi na Nigeria Alhaji Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a hukumance. Saboda haka gobe Talata 12 ga watan 2021 shine 1 ga watan Ramadan a Nigeria.

GUZURIN WATAN RAMADAN: Menene Musulmi yakamata yayi idan an ga watan Ramadan?

Daga Mahmud Isa Yola

Ya tabbata a sunnah cewa idan aka ga wata akwai addu’a da ake yi. Wannan addu’ar kuwa ita ce “Allahumma ahillahu alaina bil Amni, wal Iman, wal Salaama, wal Islam, Wat Taufiq Lima tuhibbu wa tarda, Rabbuna wa Rabbuka-Llah”. [At-Tirmidhi]

Ma’anar sa, “Ya Allah Ka Sa (wannan wata ya kasance) na samun tsaro, da Imani, da zaman lafiya, da musulunci da dacewa ga abunda Kake So, Mahaliccin mu kuma Ubangijinka Allah.”

Daga karshe yaku ‘yan uwa mu daura damara sosai na ibadaa sosai tare da ikhlasi. Mu shirya karanta Al-Qur’ani, Tarawi, Sadaka, ciyarwa, da sauran ayyuka na neman yaddan Allah.

Allah Nuna mana watan Ramadaan Lafiya, Allah Sanya mu cikin bayin Sa ‘yantattu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button