Labarai

HARIN ‘YAN BINDIGA: Al’ummar yankin Yakawada suna gudun hijira daga kauyukan su

Al’ummomin yankin Yakawada a karamar hukumar Giwan jihar Kaduna, suna ta gudun hijira daga kauyukan su zuwa cikin garin Giwa da Zariya, saboda hare-haren da ‘yan bindiga suke kai musu a kullum rana.

Kauyukan da ‘yan bindigan suka fitina dai sun hada da garin Kaya, Unguwar Namama da Doka da Garawa, Hayin Randa, Kagara, Unguwar Danyaya, Unguwar Sarki da kuma wasu kauyuka da dama duk da ke karkashin gundumar Yakawada. Sai kuma Idasu inda ‘yan bindigan suka sha kai hare-hare kwanakin baya.

Ko a satin da ya gabata ‘yan bindigan sun shiga kauyukan Doka da Garawa da Unguwar Danyaya sun kashe mutane biyu da raunata wasu, tare kuma da yin garkuwa da mutane 16, ciki kuwa har da mata masu jego da jariransu.

Yanzu haka dai wasu garuruwan da ‘yan bindigan suka addaba sun zama kufai, duk al’ummar kauyukan sun yi gudun hijira, inda wasu daga cikin al’ummar kauyukan suke zaman dardar, ba su yin barci a gidajen su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button