Labarai

Fulani makiyaya sun kaddamar mummunan hari a jihar Ogun


An labarto cewar makiyaya sun shiga kauyen Owode Ketu sun kai wa mutanen garin hari da misalin qarfe biyar na safiyar jiya Alhamis. Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, dan majalisa mai wakiltar al’ummar Ketu a majalisar dokokin jihar, Hon. Wahab Haruna Abiodun, ya ce abun takaici ne damuwa matuka yadda aka zubar da jini a garin Ketu.

A cewar sa “Fulani makiyayan sun kai hari kauyen Owode Ketu da ke gundumar Eggua, kuma sun kashe akalla mutane shida tare da raunata wasu da dama”.

“Hakika wannan abun Allah-wadai ne, kuma bai yi wa mutane dadi ba. Ya kuma ce wannan shi ne babban harin da makiyayan su ka kai su daruruwa kwanaki kadan da zuwan Sunday Igboho garin” inji shi.

Abiodun ya yi kira ga Gwamnan jihar Dapo Abiodun ya shaida wa kwamishinan ‘yan sandan jihar da sauran jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa don gudun yaduwar fitinar.

“Wannan shi ne lokacin da mu ka fi bukatar jami’an Omotekun su fito su bai wa ‘yan sanda goyon baya”.

Abun dai ya faru ne kwanaki hudu bayan kashe wani manomi Dele Olowoniyi da ake zargin Fulani makiyaya ne su ka yi a garin Yewa cikin jihar ta Ogun.

Jaridar Daily Post ta ce manomin Dele Olowoniyi an yi masa yankan rago ne a kauyen Oha a yankin Imeko da misalin karfe 1:30 na daren ranar Lahadi. Sai dai har lokacin da ake hada rahoton Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi bai dauki wayar sa ba don jin ta bakin sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button