Labarai

Har yanzu dai goguwar tsige Donald Trump na kadawa

Har yanzu dai ana ta yunkurin ganin an tsige tsohon shugaban kasar Amurka Donald J Trump wanda ake ganin shi ya dauki nauyin tada tarzoma da afkawa har cikin ginin Capitol inda ‘yan majalisar dokoki suke gudanar da zaman su don ganin an dagula sakamakon zabe.

‘Yan jam’iyyar Democrats ta shugaban kasar da ya yi nasara a zaben sun ce Donald Trump shi ne shugaban kasa na farko da ya rusa tsarin dokokin kasar shekaru 232 bayan samuwar White House na Amurka yayin da ya tura mutane cikin gidan don tayar da tarzoma a ranar 6 ga watan Janairu.

Sau biyu kenan dai ‘yan majalisun dokokin Amurka suna tsige shugaba Trump a watan da ya gabata, bayan magoya bayan sa sun tada rikicin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane.

Idan ba a manta ba kafin a rantsar da zababben shugaban kasar Joe Biden, wata ‘yar majalisa Ilhan Omar ta rubutawa majalisa takardar tsige shugaba Trump kwanaki kadan kafin barin shi a kujerar, wanda hakan ya tayar da hankalin magoya bayan jam’iyyar Republican.

Har yanzu dai za a iya cewa dambarwar ba ta kare ba, domin an ci gaba da yunkurin tsige shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button