Dan majalisar wanda ke wakiltar Abia ta Arewa da ta Kudu a majalisar dokoki ta tarayya Ossy Prestige ya mutu ne ranar Litinin sakamakon rashin lafiya da ya sha fama da ita.
Shi dai dan majalisar wanda ya ci zabe a karkashin jam’iyyar APGA ya mutu yana da shekaru 56 a duniya.
Mai magana da yawun ‘yan majalisun dokoki na tarayya, Benjamin Kalu shi ya tabbatar da hakan a ta bakin iyalan mamacin.
Mista Ossy Prestige ya mutu ne a wani asibiti da ke Germany