Malaman Jinya na gudanar da zanga-zanga kan juyin mulki a kasar Myanmar

Jami’an ‘yan sandan kasar Myanmar janye da tankokin ruwan zafi suna watsawa masu zanga-zanga a babban birnin kasar ta Myanmar ranar Litinin din nan a yayin da dubban mutane suka shiga zanga-zangar da a yau ta shiga kwanaki na uku, domin nuna rashin amincewa da hambarar da gwamnatin zababbiyar shugabar kasar Aung San Suu Kyi da sojoji suka yi a ranar Litinin din makon jiya

Kasashen duniya sun yi Allah-wadai da wannan juyin mulki da sojoji suka yi a kasar Myanmar, ciki kuwa har da kasar Amurka da ke bin tafarkin farar hula.

Wata malamar jinya da ke aiki a asibitin Gwamnati yayin gudanar da zangar-zangar a babban birnin Yangon, Aye Misan ta ce “A matsayin mu na jami’an lafiya, mun jagorancin wannan yaki ne domin kira ga dukkan jami’an gwamnati da su shigo cikin wannan zanga-zanga don yakice gwamnatin soji a qasar”,

Ta kara da cewa “Muna son mutane su san cewa ba ma tare da gwamnatin soji da kuma dukkan manufofinta, saboda haka dole mu tashi tsaye don kawo sauyi”.

Leave a Reply

Your email address will not be published.