Labarai

Sabuwar Cutar Annobar Ebola Ta Sake Bulla Jamhuriyar Kongo

Ma’aikatar lafiya ta jamhuriyar Kongo ta ce wata nau’in sabuwar annobar cutar Ebola ta sake bulla a gabashin kasar kusa da birnin Butembo, har ta yi ajalin wata mata da ke dauke da cutar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a ranar Lahadi.

An samu matar ne dauke da alamomin annobar mai saurin cinye rayuwar mutane a garin Buena tun ranar 1 ga watan Febreru, amma ta mutum a wani Asibiti da ke birnin Butembo kwana biyu da kwantar da ita. Matar dai tana auren wani mutum ne da ya taba kamuwa da cutar tun bullar annobar na baya.

Yanzu haka dai hukumar da ke kula da cututtuka masu yaduwa a kasar suna cigaba da aiki don ganin an dakile yaduwar annobar ta Ebola.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button