Album/EPLabarai

Uwargida ta kashe amaryar da mijinta zai aura ana saura kwana 3 aure

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata matar aure, Suwaiba Shuaibu a bisa zarginta da kashe budurwar da mijinta zai aura, Aisha Kabir ana sauran kwanaki 3 a daura aurensu.

Suwaiba ta shaidawa yan sanda cewa ta kira yarinyar da mijin nata zai aura ne a waya cewa tanason su hadu zata bata gudunmuwar biki.

Manuniya ta ruwaito ita Amaryar da ake shirin Aura batasan da wa take magana ba, amma dai daga baya ta amince suka hadu, sai Suwaiba ta shammaci Amaryar da mijin nata ke shirin Aura Aisha ta ja ta wani kango ta inda kan tayi aune ta zaro wuka ta soka mata a kirji da wuya da sauran sassan jikinta har a karshe dai amaryar ta mutu.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Gimawa dake karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button