Addini da RayuwaAlbum/EPHausa SongsLabarai

Kaduna zata mayar da yara dari 160 garuruwansu da ta ceto a wata tsangaya

Kaduna za ta mayar da yara dari 160 garuruwansu da ta ceto a wata tsangaya

Gwamnatin jihar Kaduna ta ceto yara kanana 160 wadanda mafi yawansu yan asalin wasu jihohi ne da kuma bakin haure da aka kangesu a wata haramtacciyar tsangaya a wani yanki na jihar.

Daga cikin su akwai ‘yan jihar Kebbi guda 16, Abuja 2, Kano 15, Katsina 15, Zamfara 8, Sokoto 1, Nasarawa 12, Neja 5, Kwara 4, Kogi 2, Oyo 2, Kaduna 68 sai kuma yara bakin haure daga kasashen Nijar (5), Burkina Faso (3) da Benin (1).

Mataimakiyar Gwamnan Kaduna tare da wasu yara

A wata sanarwa da Gwamnatin jihar ta fitar ta ce ba zata zura ido aga ana cin zarafin yara da sunan bara ba “don haka an killace yaran a wani wuri ana duba lafiyarsu kafin daga bisani a mayar dasu gidajensu ko garuruwansu na asali”

Rahotanni sun nuna cewa tun daga watan Maris, 2020 zuwa yanzu, gwamnatin Kaduna ta kama yara almajirai kimanin dubu 31,092, inda ta mayar da su zuwa jihohin su, tun bayan da gwamnonin Arewa suka kudiri aniyar dakile cin zarafin da ake yi wa yara da sunan almajiranci. Wanda kuma tun daga wannan lokacin ne gwamnatin ta dukufa wajen zakulo irin wuraren da ake kange yara tana ceto su tana mayar da su wurin iyayensu domin ci gaba da neman ilmi a gabansu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button