
Gobara ta kashe uwa da ‘yayanta guda Biyu a kauyen Riban Garmu, dake mazabar Dewu Ward cikin karamar hukumar Kirfi ta jihar Bauch.
Mutum hudu sun samu kuna a inda aka kwashesu zuwa babban asibitin garin, Kirfi General Hospital.
Manuniya ta ruwaito lokacinda gobarar ta tashi a gidan mai dakuna hudu ana ji ana gani uwa da ‘yayan nata suna ihun neman agaji amma an kasa balla kofar a cirosu har suka babbake gidan kuma ya kone kurmus. Ana dai zargin tartsatsin wutar lantarki ce ta haddasa wutar.
A gefe daya kuma dan majalisar jiha mai Wakiltar Kirfi, Abdulkadir Dewu, ya kai ziyarar ta’aziyya da jaje ga al’ummar da abun ya faru a madadin Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed.
Dan majalisar ya baiwa iyalan gudunmawar Naira 250 a madding Gwamnan.