Labarai

DA DUMI-DUMI: Za a koma makaranta 18 ga watan Janairu kamar yadda aka tsara tun farko –inji Ministan ilimi

Ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya ce bayan kammala tattaunawa da tuntubar masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi a bar ranar 18 ga watan Janairu 2021 a matsayin ranar komawa duka makarantu a Nigeria

Manuniya ta ruwaito Ministan ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi, Bem Goong ya fitar da yammacin yau Alhamis

Sanarwar ta ce an fasa batun sauya ranar komawar bayan zama da akayi da masu ruwa da tsaki amma dai za a sanya ido sosai domin a tabbatar da ana bin dokokin kariya daga kamuwa da cutar korona a duka makarantu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button