Labarai

An yi garkuwa da yan kasuwar Kano su 27 a hanyar zuwa saro kaya

Yan bindiga sun yi garkuwa da yan kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano mutum 27 a hanyarsu ta zuwa sarin kaya a garin Aba ta jihar Abia

Rahotanni sun nuna an sace yan kasuwar ne a daidai garin Okene dake jihar Kogi ranar Lahadi.

Da farko dai masu garkuwar sun nemi a biyasu Naira miliyan 45 kan mowane dan kasuwa guda daya kafin daga bisani aka sauko zuwa Naira miliyan 27 kudin fansan dukansu (miliyan 1 kowane dan kasuwa daya).

Majiyar MANUNIYA ta ruwaito kakakin yan kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano, Mansur Haruna, ya ce cikin yan kasuwa 27 din akwai yan kasuwa daga Kofar Wambai, da Sabongari da sauran kasuwannin Kano da suka hadu domin zuwa saro kayan.

Kawo yanzu dai yan kasuwan sun ce sun dukufa yin sadaka da addu’oi akan Allah ya kubutar dasu kanan kuma sun roki Gwamna Ganduje da ya tallafa wajen ganin an kubutar da yan kasuwar “domin galibinsu kananan yan kasuwa ne wadanda jarinsu bai fi Naira dubu 400 ba” inji Haruna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button