Album/EPLabarai

An sanya dokar kayyade kayan lefe da gara a jihar Jigawa

A kokarin saukaka aure tsakanin ‘yan mata da samari hukumomin garin Kanya dake jihar Jigawa sun fitar da wasu hanyoyin kayyade wasu abubuwan al’ada da ake yi.

Ciki har da dokar da ta tanadi a yi matsakaicin  akwati guda daya mai dauke da atamfofi hudu, leshi daya, shadda daya, gyale daya, hijabi biyu, takalmi da jakar hannu guda daya, kayan kwalliya da sauran ‘yan tarkacen da za a hada cikin wannan akwati.

Dokar ta kuma bukaci a kai kayan lefen wurin daurin aure a gaban waliyyan amarya da ango, da mahukunta da sauran jama’a domin tabbatar da an kiyaye dokar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button